23 Mayu 2022 - 16:30
WHO Na Taron Gaggawa Game Da Barkewar Kyandar Birai A Turai

Hukumar lafiya ta duniya za ta gudanar da taron gaggawa domin tattaunawa game da barkewar cutar kyandar birai a turai.

Wannan na zuwa ne bayan samun sama da mutane 100 da aka tabbatar ko ake zargin sun kamu da cutar a Turai a baya-bayan nan.

A wani abu da Jamus ta kira barkewa mafi girma a Turai, an tabbatar da samun wadanda suka kamu da cutar a akalla kasashe 5 da suka hada da Biritaniya da Spain da Portugal da Jamus da Italiya, har ma da Amurka da Canada da Australia.

Cutar wadda aka fara gano ta a tsakanin birrai dake yaduwa ta hanyar mu’amala, ba kasafai ake samunta a wajen nahiyar Afrika ba, don haka, batun ya zama abun damuwa.

Sai dai, masana kimiyya ba sa tsammanin barkewar cutar za ta zama annobar duniya kamar COVID-19, bisa la’akari da cewa, kwayar cutar ba ta da saukin yaduwa kamar ta COVID-19.

342/